4 Afirilu 2022 - 19:24
Kasashen Iran da Siriya Sun Tattauna Game da Hanyoyin Bunkasa Hulda Ilimi Tsakaninsu

Jakadan kasar iran a birnin Damaskas na kasar Siriya ya gana da ministan Ilimi na kasar siriya inda suka tattauna game da hanyoyin da za’a bi wajen ganin an bunkasa huldar Ilimi tsakanin kasahen biyu da kuma musayar kwarewa da goyayya da bangarorin biyu suke dashi da kuma kara yawan adadin musayar daliban kasashen juna.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Anasa bangaren jakadan iran a siriya Mahdi Subhani ya yi ishara game da ci yalwar da tsarin ilimi yake das hi a kasar ta siriya da kuma irin rawar da yake take wa wajen gina kyakkyawar makoma , kana ya jaddada mukhimmancin karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu a bangarori daban daban musamman harkar Ilimi

Anasa bangaren ministan Ilimi na kasar Siriya Darema Taba ya bayyana irin kyakkyawan danganatakar dake tsakanin kasashen biyu , kana ya jaddada game da muhimmancin yin aiki tare wajen raya harkar Ilimi ta hanyar musayar kwarewa da suke da shi domin amfanin kasashen da bunkasa harkar ilimi.

342/